Ganawarmu ta karshe da Mandela - 'Yarsa

Image caption Makaziwe Mandela

A daidai lokacin da Majalisar dokokin Afruka ta Kudu ke wani zama na musamma domin karrama Marigayi Nelson Mandela, Babbar 'yarsa, Makaziwe, ta yi tsokaci kan ranakun karshe kafin mahaifinta ya rasu a ranar Alhamis.

A wata hira da BBC, Makaziwe ta ce da koda yake da kyar mahaifin nata ke iya bude idanunsa, amma ta tabbatar cewa ya ji duk maganganun da iyalansa ke yi suna ce masa suna kaunar shi matuka.

Ta ce duk da cewa akwai 'yar rashin fahimtar juna tsakaninta da mahaifinta a 'yan shekarun da suka wuce, amma babban fatan Mr Mandela, shi ne a samu sassantawa a tsakanin iyalansa.

Makaziwe ta ce babban abun da mahaifinta ya koya ma ta da ma duniya baki daya, shi ne karfin hali na yafewa.

Karin bayani