Majalisar Afrika ta kudu za ta karrama Mandela

addu'o'in makokin Mandela
Image caption Addu'o'in makokin Mandela

Majalisar dokokin Afrika ta kudu za ta gudanar da zama na musamman domin karrama Nelson Mandela yayinda shugabannin kasashen duniya ke shirin halartar addu'o'in da za'a gudanar ranar Talata.

Zaman dai na zuwa na a farkon makon da aka ware na tunawa da marigayin kafin binne shi ranar 15 ga Disamba.

Tsohuwar matar Mandela, Winnie Madikizela-Mandela da jikansa Mandla wakilai ne a cikin majalisar sai dai babu tabbas ko za su halarci zaman na musamman.

Kimanin shugabannin kasashen duniya 60 ne ake sa ran za su halarci jana'izar ko kuma addu'o'in da za'a gudanar ran Talata.