'Masu kudi ne ke amfana da Nigeria'

Image caption Dr Ngozi Okonjo Iweala

Ministar Kudin Nigeria, Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewar masu hannu da shuni ne ke cin ribar bukasar tattalin arzikin kasar kuma ci gaban ba ya samar da guraben ayyukan yi.

Ministar ta bayyanawa wani taron shugabannin 'yan kasuwa a Nigeria cewar tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba da kashi 6.7 a cikin 100.

Kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya bayyana, tsohuwar manajan darektar bankin duniya din ta kara da cewar kiyasi ya nuna cewar an samar da guraben ayyukanyi miliyan daya da dubu 600 a cikin watanni 12 a kasar, amma kuma ayyukan yi na ci gaba da karanci a tsakanin al'ummar Nigeria.

A cewarta "Ina tunani ya kamata ci gaba tattalin arzikinmu ya kai kashi 10 cikin 100 a duk shekara domin samar da isassun ayyukan yi a tsakanin a'umma."

Nigeria ce kasar da ta fi kowacce samar da danyen man fetur a Afrika kuma ana hasashen cewar karfin tattalin arzikinta zai zarta na kasar Afrika ta Kudu a 'yan shekaru masu zuwa.

Karin bayani