An cafke karuwan Najeriya a Nijar

'Yan Nijeriya a Delhi
Image caption 'Yan Nijeriya a Delhi

Hukumar yaki da Safarar Bil adama a Najeriya (NAPTIP) ta ce ta karbi wasu 'yan mata 17 'yan asalin kasar da ake zargin cewa karuwai ne da hukumomin Nijar suka kama a cikin kasar suna shirin tsallakawa zuwa Turai domin sana'ar ta Karuwanci.

Rahotanni sun ce 'yan sandan Nijar din ne suka kama su lokacin da suka kai samame kan wani sansanin da suka kafa a inda suka yada zango cikin yankin Agadez.

Jumhuriyar ta Nijar dai ta kara kaimi wajen hana bakin haure bi ta cikin kasar bayan wasu mutane sama da 90 sun rasa rayukansu sakamakon yunwa da kishin ruwa a hamadar Sahara, lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa kasar Algeria.

Malam Hassan Tahir shi ne Kwamandan Hukumar a shiyyar Sokoto na hukumar ta NAPTIP wanda aka mikawa 'yan matan. Ya kuma yi bayanin irin yadda 'yan matan suka amsa cewar maza masu yawa na kwanciya da su a kowacce rana.

Karin bayani