Facebook ya kirkiro madannin tausayawa

Sabon madannin Facebook
Image caption Sabon madannin Facebook

Dandalin sada zumunta na Facebook ya kirkiro wani sabon madannin "tausaya" da zai maye gurbin madannin "so" ko kuma "like" a Turance.

Idan mai amfani da shafin ya zabi alamar da ke nuna bakin ciki ko bacin rai a lokacin da ya ke rubuta wani labari, sai madannin "so" (like) ya koma "tausaya" (sympathise).

Wani injiniyan Facebook ya ce an kirkiro fasahar ne saboda korafe-korafen da wasu daga cikin masu amfani da shafin ke yi.

Sai dai kuma ya ce za'a dau lokaci kafin kaddamar da sabon madannin ga ma'abota shafin.

Ganawa da masoya

A wata ganawa da masoyan Facebook, wani mahalarcin taron ya yi tambaya game da yiwuwar sauya madannin "so" (like) idan hakan bai dace da labarin da mutum ya rubuta ba, kamar ace ya bada labarin rasuwar iyayensa.

Wani injiyan manhajar kwamfuta a Facebook Dan Muriello ya ce tuni kamfanin ya riga ya kirkiro wannan madanni.

Ya ce; "Mutane da dama sun bayyana farin cikinsu da samun wannan sabon madanni sai dai mun yanke hukuncin cewa ba yanzu ya kamata mu fara amfani da shi ba."

Kamfanin Facebook kan gana da masoyansa akai-akai domin jin ra'ayoyinsu game da yadda za'a inganta dandalin.

Sanadiyyar irin wannan ganawar ne kamfanin ya samar da hanyar aika sako ta Facebook da kuma tsarin tallatawa mai amfani da shafin wasu mutane da aka fuskanci yana da dangantaka da su don ko za su kulla abota.