Nelson Mandela: Ko kun san?

Nelson Mandela.
Image caption Nelson Mandela.

Nelson Mandela shararren mutum ne wanda al'ummar duniya ta san abubuwa da yawa na gwagwarmayar rayuwarsa. Sai dai ga wasu abubuwa guda shida wadanda ba lallai bane ace kun san su game da marigayi tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu.

1. Masoyin wasan dambe ne. Lokacin kuruciyarsa Mandela kan yi dambe da tsere mai nisan zango. Ko cikin shekaru 27 da ya kwashe a jarun, ya kan motsa jikinsa kullum. Daga cikin abubuwan da ake nunawa a gidan adana tarihin iyalin Mandela dake Soweto har da kambun damben duniya da dan damben Amurka Sugar Ray Leonard ya baiwa Mandela.

2. Nelson ba sunan yankansa bane. Rolihlahla Mandela na da shekaru tara lokacin da wani malami a makarantar firamare ta mishan da ke Qunu, Afrika ta kudu ya rada masa sunan Nelson bisa al'adar radawa 'yan makarantar boko sunan turawa. Sunansa na ainahi Rolihlahla na nufin "dan rikici" a harshensu na Xhosa. Amma mafi yawan mutane a kasarsu na kiransa da sunan iyalinsu - Madiba - saboda girmamawa.

Image caption Dubban 'yan Afrika ta Kudu

3. Amurka na daukarsa dan ta'adda har 2008. Gwamnatin Ronald Reagan ce ta sa sunan Mandela tare da sauran jagororin ANC cikin 'yan ta'adda bayanda gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu ta kira ANC kungiyar 'yan ta'adda. Kafin 2008 duk lokacin da Mandela da jagororin ANC za su Amurka sai sun nemi alfarmar ma'aikatar hulda da kasashen waje ta Amurkan.

4. Ya manta tabaronsa a kurkuku. Ranar 11 ga Fabrairu 1990 aka sako Mr Mandela daga kurkuku bayan kwashe shekaru 27 a tsare. Bayan sakinsa, an kai Mandela da matarsa ta wancan lokaci Winnie zuwa tsakiyar birnin Cape Town domin yin jawabi ga dimbin magoya bayansa. Sai dai lokacin da ya ciro jawabinsa zai karanta sai ya ga ashe ya manto tabaronsa a kurkuku don haka sai na Winnie ya ara ya karanta jawabin.

Image caption Addu'o'i kan Mandela

5. Ya sha bad da kama domin kaucewa kamu. Bayan da ya yi kaurin suna a gwagwarmayar ANC, an lakabawa Mandela sunan "Black Pimpernel", saboda kwarewarsa wurin bad da kama ta yi kama da labarin wani littafi mai suna "Scarlet Pimpernel", game da wani dan gwagwarmaya da ya kware wurin bad da kama. Mandela dai ya yi shigar direba, kuku, da kuma mai ban ruwan fulawa. Har yanzu ba'a san yadda aka yi 'yan sanda suka gano shi har suka kama shi ba.

6. Ya na da kamfanin aikin lauya amma ya yi shekaru babu digiri. Mr Mandela ya karanci aikin lauya a karkatse na tsawon shekaru 50 tun daga 1939, inda ya fadi a rabin kwasa-kwasan da ya dauka. Ya samu damar aikin lauya ne bayanda ya yi diploma a bangaren bayan digirinsa na farko, kuma a Agustan 1952, shi da Oliver Tambo suka kafa kamfanin aikin lauya na bakar fata na farko a kasar mai suna Mandela and Tambo. A shekarar 1989 ne dai ya samu kammala digiri a bangaren lauya.