Ana bankwanan karshe da Mandela

Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela

An fara bankwanan karshe ga tsohon Shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela a birnin Pretoria.

Ana tafiya da akwatin gawar da aka nade da tutar kasar ne a motar daukar gawa da 'yan rakiya ta ban-girma ana wucewa gaban dubun-dubatan mutane.

An shirya kai gawar ne fadar gwamnatin kasar, da hedikwatar tsohuwar Jamhuriyar Afrika ta Kudu.

Da yamma kuma mawakan Afrika ta Kudu za su yi wakoki na addu'a wadda kowa ke da damar halarta.

A jiya ne shugabanni daga kasashen duniya daban-dabam suka hadu da dubun dubatan 'yan Afrika ta Kudu a babban filin wasa na Soweto inda aka gudanar da taron girmama Nelson Mandela.

.

Karin bayani