ASUU: Gwamnati ta yi amai ta lashe

Image caption Malaman jami'o'in Nigeria na ci gaba da yajin aiki.

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce ta soke wa'adin da ta bai wa malaman jami'o'i da su janye yajin aikin da su ke ko kuma su dauki kansu a matsayin korarru.

Mashawarcin shugaban kasar na musamman kan yada labarai, Dr Doyin Okupe ya ce gwamnatin ta fasa korar malaman ne saboda da damansu sun koma bakin aiki.

Sai dai shugaban kungiyar malaman, ASUU, Dr Nasir Isah Fagge ya musanta cewa wasu daga cikin malaman sun koma bakin aiki.

Ya kuma ce dama barazanar ta gwamnati ba za ta iya tasiri ba kasancewar ta saba dokar dauka da sallamar ma'aikata ta Nigeria.

Kimanin watanni shida ke nan malaman jami'o'in Nigeria su ke yajin aiki domin neman gwamnati ta samar da kayayyakin inganta koyo da koyarwa a jami'o'in.