Gwamnati da ASUU sun cimma matsaya

Image caption ASUU ta ce sun cimma matsaya da gwamnatin Nigeria

Kungiyar malaman jami'oin Nigeria ASUU ta ce mai yiwuwa nan gaba kadan za ta dakatar da yajin aiki bayan ta cimma matsaya da gwamnatin kasar.

Shugaban kungiyar, Dr Nasir Fagge, ya shaidawa BBC cewa shugabannin kungiyar za su gudanar da taro nan gaba kadan sannan su yanke shawarar kan ranar da za su dakatar da yajin aikin da kungiyar ta kwashe watanni biyar tana yi.

Yajin aikin dai ya janyo zazzafar takaddama tsakanin gwamnatin Nigeria da malaman jami'oin, lamarin da ya sanya gwamnatin yin barazanar sallamar malaman daga aiki muddin suka ki koma wa ranar Litinin din da ta gabata.

Malaman dai sun bijirewa umarnin gwamnatin, kodayake daga baya gwamnatin ta yi ikirarin cewa kashi rabin malaman jami'ar sun koma aiki, ikirarin da malaman suka musanta.

Karin bayani