An kwantar da gawar Mandela a Pretoria

Gawar Mandela
Image caption Sojoji na shigar da gawar Mandela Union Buildings, Pretoria.

A yanzu haka gawar Nelson Mandela na kwance cikin ginin Union Buildings na Pretoria, inda aka rantsar da shi shugaban kasar Afrika ta Kudu bakar fata na farko a 1994.

An dauko akwatin gawar da aka nade da tutar kasar ne a keken doki inda 'yan sanda suka yi mata rakiya kan babura yayinda jiragen helikopta ke shawagi kan su.

Dakarun soji ne kuma suka shigar da gawar cikin ginin na Union Buildings.

Za'a bar gawar ta Mandela a cikin ginin ne zuwa kwanaki uku.

A ranar Lahadi ne kuma za'a binne gawar a kauyen Qunu dake Afrika ta Kudu.