Rashawa: kariya ga 'yan majalisar Romania

Shugaban Romania Traian Basescu
Image caption Shugaba Traian Basescu ya ce matakin ya kawar da shekaru goma na kokarin tsaftace siyasar Romania.

'Yan majalisar dokokin Romania sun kada kuri'ar amincewa da kudurin kare kansu daga tuhumar cin-hanci da rashawa.

A wani mataki da ba a taba tsammani ba, wanda Hukumar Kungiyar Kasashen Turai da ofishin jakadancin Amurka a Bucharest babban birnin kasar su ka yi Alla-wadai da shi, majalisar wakilan kasar ta amince da kudurin bayan wani taron sirri na kwamitinta na shari'a.

A halin yanzu 'yan siyasa 28 ne da suka hada da ministoci da tsohon framinista ke fuskantar shari'a ko zaman gidan yari kan laifukan rashawa.

Sakamakon wannan mataki wadanda ke zaman gidan kaso yanzu za a sake su.

Shugaban kasar wanda ke sukan lamirin hadakar jam'iyyun da ke mulki ya ce matakin ya kawar da shekaru goma na kokarin tsaftace siyasar Romania.