Uruguay ta halatta tabar wiwi

Fadar gwamnatin Uruguay
Image caption Fadar gwamnatin Uruguay

Uruguay ta zamo kasa ta farko a duniya da ta halatta amfani da tabar wiwi don nishadi amma gwamnati za ta kayyade yadda za a rinka kasuwancinta.

Bayan shafe tsawon sa'oi 12 ana tufka muhawara, Sanatoci sun kada kuri'a da rinjayen kuri'u 16 a kan goma 13 na wadanda suka goyi bayan dokar ta gwamnati wadda ta halatta ma 'yan kasar ta Uruguay sayarwa da nomawa da kuma shan tabar wiwi.

Sanata Roberto Conde na gwamnatin kawance ta kasar ya ce dokar za ta kawar da matsalar da yanzu ake fama da ita.

Yace, "An kafa dokar shan tabar ta wiwi ne don ta kawar da munanan matsalolin da shanta ke haddasawa a cikin al'umma."

Sauye-sauyen dai ba za su fara aiki ba sai bayan watan Aprilun shekara mai zuwa.

Za a kyale 'yan kasar ta Uruaguay da suka zarta shekaru 18 da aka yi ma rajista su sayi har zuwa gram 40 na tabar wiwi a cikin wata daya. Sai dai kuma ba za a sayarwa baki ba.

Karin bayani