An kori ma'aikatan lafiya 400 a Zamfara

Image caption Gwamnatin ta ce ma'aikatan sun bijire wa doka

Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta ba da sanarwar sallamar ma'aikatan jinya da ungozomomi sama da 400 da suka shiga wani yajin aikin da kungiyarsu ta kira.

Gwamnatin jahar dai ta ce yajin aikin ya saba doka don haka daidai yake da barin wurin aiki ba tare da izini ba.

Sai dai ma'aikatan lafiyar sun yi fatali da sanarwar korar tasu a zaman barazanar wofi.

A ranar Laraba ta makon jiya ne dai ma'aikatan lafiyar suka shiga yajin aiki na har illa masha Allahu sakamakon abin da su ka kira gazawar gwamnatin jihar ta biyansu da sabon tsarin albashin ma'aikatan lafiya da aka fi sani da CONHESS.

Karin bayani