An soke auren jinsi a Australia

Image caption Gwamnatin Australia ta haramta auren jinsi a kasar

Kotun kolin kasar Australia ta soke dokar da ta ba da damar auren jinsi daya a babban birnin kasar Canberra da yankunan da suke kewayensa.

A watan Oktoba ne majalisar yankin ta amince da dokar auren jinsi dayan, amma kuma gwamnatin tarayyar kasar ta kalubalanci dokar, da cewa ta saba wa dokarta ta aure.

A karshen makon da ya gabata ne dai aka yi auren 'yan jinsi daya na farko a kasar ta Australia a birnin na Canberra, inda aka daura aure kusan 30, da suka hada da na wani dan siyasa na bangaren adawa da abokin mu'amularsa.

Sakamakon hukuncin kotun kolin na yanzu dukkanin auren da aka daura din za a soke su.

Karin bayani