Hukuncin kisa kan malami a Bangladesh

Image caption Abdul Kader Mullah

Kotun kolin Bangladesh ta amince da hukuncin kisan da aka yanke wa shugaban 'yan adawa na masu kishin Islama, saboda laifin cin zarafin bil adama lokacin yakin kwatar 'yancin kan kasar daga Pakistan a shekarar 1971.

Abdul Kader Mullah, wanda kusa ne a jam'iyyar Jamaat-e-Islama an dakatar da aiwatar da hukuncin kisa a kansa a ranar Talata saboda daukaka karar da ya yi kafin ya gamu da cikas a kotun koli.

Babban lauyan gwamnati, Mahboub e Allam ya shaidawa BBC cewar a yanzu an gama takaddama a kan shari'ar, amma kuma shugaban kasa zai iya yafe masa.

A farkon wannan shekarar an yanke wa shugabannin masu kishin Islama da dama hukuncin kisa a Bangladesh kuma a kan Abdul Kader Mullah ake shirin soma aiwatar da hukuncin kisan.

An tsaurara matakan tsaro a Dhaka babban kasar da kuma daukacin kasar saboda wannan hukuncin.

Karin bayani