Farashi daidai mutunci a Faransa

Image caption Farashinka daidai da mutuncinka

Wani shagon sayar da gahwa a Faransa ya fito da tsarin sakawa abokan huldarsa masu mutunci ta hanyar bambanta farashin hajarsa.

A tsarin shagon, wanda ya tsaya aka gaisa kana ya yi murmushi kafin ba da odar kofin gahwa, farashinsa shi ne Euro guda amma wanda ya ba da oda kai tsaye farashinsa Euro bakwai.

Mai shagon, Fabrice Pepino ya ce da wasa ya fara wannan tsarin amma yanzu ya na ganin amfaninsa don kuwa abokan cinikinsa na mutanta shi da kyau.

Mr Pepino ya ce; "Mutane kan zo nan a gajiye kuma su kan yi mana rashin mutunci yayinda suke ba da oda."

Ya kara da cewa shi ma a intanet ya gano wannan dabarar kuma shi kam lalle ta biya shi.