'Nigeria ta kawar da kai daga kisan gilla'

Image caption Wasu daga cikin wadanda aka kashe a rikicin Jos

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa-Human Rights Watch, ta zargi hukumomin Nigeria da kawar da kai daga kisan gilla da aka yi a rikicin kabilanci a jihohin Filato da Kaduna.

Mutane kusan 3,000 ne aka kashe a tashin hankalin tsakanin Musulmai da Kiristoci.

A cewar kungiyar duk da cewar mutane da dama sun kai kara wajen 'yan sanda a kan cewar an kashe musu 'yan uwa, amma kawo yanzu babu wanda aka hukunta.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta gana da mutane 180 daga jihohin Kaduna da Filato inda aka yi rikicin tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai 'yan sanda sun musunta zargin.

Karin bayani