"Maharan Kenya ba su mutu ba"

Image caption Fiye da mutane 60 ne suka mutu a harin Westgate, Kenya.

'Yan sanda a New York sun musanta bayanan da mahukuntan Kenya suka yi game da makomar wadanda suka kai hari a kan rukunin kantunan Westgate, inda suka ce mai yiwuwa sun tsira da rayukansu.

Hukumomin tsaron Kenya dai sun ce baki daya maharan, 'yan kungiyar masu kishin Islama ta al Shabaab, sun mutu a harin da suka kai a Nairobi cikin watan Satumba, wanda ya hallaka mutane fiye da 60.

Hukumar 'yan sandan New York ta aike da 'yan sandan ciki da dama zuwa Nairobi domin bincike kan harin.

Sun kuma ce matar nan 'yar Britaniya Samantha Lewthwaite da aka ce ita ta jagoranci harin, babu wata alama da ta nuna ta shiga rukunin kantunan duk da rahotannin da wasu jaridu suka bayar a Britaniya.