Nigeria na sakaci da rikice-rikice - HRW

Image caption Daruruwan mutane na mutuwan a rikicin kabilanci a Nigeria.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta zargi hukumomin Nigeria da rashin daukar mataki game da rikice-rikicen addini da kabilanci da ake fama da su a tsakiyar kasar.

Kimanin mutane 3,000 ne suka rasu a rigingimun da su kan barke tsakanin Musulmi da Kirista.

Kungiyar ta ce duk da yake kungiyoyi da yawa sun kai kukansu ga 'yan sanda, da wuya a samu wanda aka taba shigar da kararsa dangane da rikice-rikice.

HRW ta ce ta tattara ra'ayin mutane 180 ne a jihohin Kaduna da Plateau wanda suke yankin tsakiyar Nigeria.

Sai dai 'yan sanda sun musanta wadan nan zarge-zarge.