An kashe kawun shugaban Korea ta Arewa

Jang Song Thaek
Image caption A farkon makon nan ta talabijin aka ga jami'an tsaro sun yi awon gaba da shi yayin taron jam'iyyar ma'aikata da ke mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa ya ba da sanarwa aiwatar da hukuncin kisa a kan kawun shugaban kasar wanda a da yake da matukar ikon fadi a ji Jang Song Thaek.

Sanarwar ta ce an zarge shi ne da laifin aikata abin da ya saba wa ikonsa da aikata wasu abubuwa na adawa da juyin juya halin kasar da kuma halayyar da ba ta dace ba.

An yi masa shari'a ne a wata kotun soji ta musamman kuma nan take aka aiwatar da hukuncin kisan a kansa, a matsayin maci amanar kasa.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta ce labarin kisan idan ya tabbata gaskiya, na nuna irin tsananin rashin imanin gwmanatin Korea ta Arewa.

Rahotanni daga Korea ta Kudu sun ce gwamnatin kasar ita kuma ta na wani taron ministocin tsaro domin tattauna lamarin makwabciyar tata.

Karin bayani