Majalisar wakilan Amurka ta amince da kasafin kudi

John Boehner
Image caption A mako mai zuwa ne majalisar dattawa da 'yan Democrat ke da rinjaye za ta kada kuri'a a kan kudurin kasafin kudin.

Majalisar wakilan Amurka da 'yan jam'iyyar Republican ke da rinjaye ta amince da kudurin kasafin kudin kasar na shekara biyu.

'Yan jam'iyyar da kuma na Democrat sun cimma matsaya a kan kudurin wanda aka tsara domin gudun sake fadawa dambarwar kudin da kasar ta tsunduma ciki da ta yi sanadiyyar rufe wasu ayyukan gwamnati na tsawon makwanni biyu a watan Oktoba.

Kasafin ya samu gagarumar karbuwa bayan da jagoran 'yan Republican a majalisar, John Boehner, ya bukaci 'yan ra'ayin rikau masu dari-dari , wadanda suke son ganin an rage gibin kasafin kudin kasar sosai, su mara baya ga kasafin.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai bayan kada kuria'r , Mr Boehner ya soki lamirin masu adawa da kudurin.

A mako mai zuwa ne ita kuma majalisar dattawa da 'yan Democrat ke da rinjaye za ta kada kuri'a a kan kudurin kasafin kudin.