Winnie ta bayyana alhinin mutuwar Mandela

Image caption Tsohuwar Matar Mandela Winnie na alhinin mutuwarsa

Tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela, Winnie Madikizela-Mandela ta yi bayanin yadda ta kasance da tsohon mijin nata har zuwa lokacin da ya rasu.

Winnie Mandela, ta ce ta ji cewa ta samu wata martaba da albarka yadda ta kasance a kusa da shi har lokacin da ya cika, a makon da ya wuce.

Winnie Mandela ta ce ta zauna tare da tsohon mijin nata tsawon sama da sa'oi uku har zuwa lokacin da ya yi numfashinsa na karshe.

Ta ce a duk tsawon wannan lokaci ba sa'ad da hankalinta ya tashi ta ji ba dadi, sai lokacin da sojoji suka zo suka dauki gawarsa daga nan ne ta ce ta san ya tafi ke nan.

Dubban masu ta'aziyya ne dai suka yi layi domin yi wa gawar tsohon shugaban Afrika ta Kudun bankwana a Pretoria, inda za a ci gaba da ajiye gawar a rana ta uku yau Juma'a domin yi mata bankwana.

Karin bayani