Farashin mota zai nunka a Nigeria

Image caption Karin haraji zai sa mota ta gagari talakawan Nigeria

A Najeriya makonni kadan ne suka rage a fara amfani da sabon tsarin haraji kan motoci kwance da ake shigo da su kasar.

Harajin dai zai fara ne a watan Janairun shekara mai zuwa wanda za a rika cazar kaso 60 na kudin da aka sayo mota kwance.

Hakan na nuna farashin motoci zai iya nunkawa a Nigeria.

Tuni wasu 'yan kasar suka fara kukan cewa idan aka fara amfani da tsarin mota za ta fi karfin talaka a kasar.

Gwamnatin Najeriyar dai ta amince da wata sabuwar manufar kasa ta bunkasa kera motoci da harhada su a cikin gida, wanda daga ciki ne aka kara harajin da ake biya na shigo da motoci kwance dan rage shigo da su.

Wasu masu sayar da motoci dai na cewa matukar aka fara amfani da sabon tsarin, to za a kara yawan shigar da motoci kasar ne ta bayan fage.

Karin bayani