PDP ta bukaci kotu ta kori gwamnoni

  • 13 Disamba 2013
Biyar daga cikin gwamnonin sabuwar PDP sun koma APC.

Jam'iyyar PDP da ke mulkin Nigeria ta bukaci kotu ta karbe kujerun gwamnoni biyar na tsagin sabuwar PDP da suka koma jam'iyyar adawa ta APC tare da mika mukamaan ga mataimakansu idan ba su bi su zuwa sabuwar jam'iyyar ba.

A cewar lauyan da ya shigar da kara a madadin jam'iyyar, wajibi ne gwamnonin su bar mukamansu kasancewa jam'iyya ake zaba ba mutum ba.

Gwamnonin dai sun hada da Rotimi Amaechi na Rivers, Rabiu Musa Kwankwaso na Kano, Murtala Nyako na Adamawa, Magatakarda Wamakko na Sokoto da Abdulfatai Ahmed na Kwara.

Amma jam'iyyar APC PDP ba ta da hujjar shigar da wannan kara kasancewar a baya gwamnoni da dama da aka zaba a wasu jam'iyyu sun fita sun koma PDP ba tare da ajiye mukamansu ba.

Sai dai masu nazarin al'amuran siyasa a Nigeria na cewa da gangan PDP da shigar da karar a wannan lokaci don ta karkatar da hankulan 'yan kasar daga batun kakkausar wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aike wa shugaba mai ci Goodluck Jonathan.