Dalibi ya harbi 'yan makaranta a Amurka

Image caption Dalibi ya raunata dalibai a harbin bindiga

'Yan sanda a jihar Colarado ta Amurka sun ce wani dalibi ya kashe kansa a wata makarantar gaba da firamare bayan ya harbi wasu 'yan uwansa dalibai su biyu wanda daya daga cikinsu ya samu mummunan rauni.

Lamarin ya faru ne a garin Centennial da ke kudu da Denver.

Babban jami'in 'yan sandan garin Grayson Robinson ya ce da alamu dan bindigar ya je makarantar ne da 'yar karamar bindiga da nufin harbin wani malami, wanda ya gudu a lokacin., shi kuma da alamu ya kashe kansa..

Harin dai ya faru ne a jajiberin shekara daya da mummunan harin nan da wani dan bindiga ya kai a makarantar firamare ta Sandy Hook a Conncticut inda ya hallaka yara 20 da manya 6.

Karin bayani