Kumbon China ya sauka a duniyar wata:

Saukar Kumbon kasar China a Duniyar Wata
Image caption Saukar Kumbon kasar China a Duniyar Wata

Kasar China ta ce Kumbonta ya samu nasarar sauka a duniyar wata,wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba a fannin shirinta na sararin samaniya.

A hotunan da aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na kasar, an yiwa masana kimiyya dake aiki a cibiyar sarrafa kumbon dake birnin Beijing bayan aka nuna saukar Kumbon.

Kumbon dai yana dauke ne da na'ura mai kafofi shida da zata yi kokarin gano wasu sabbin abubuwa a duniyar wata.

Idan dai komai ya gudana kamar yadda aka tsara wannan zai zama karon farko cikin shekaru arba'in da aka aika kumbon.

China dai tana matukar tunkaho da wannan shiri na ta.