An kashe sojojin kiyaye zaman lafiya biyu a Mali

Dakarun kiyaye zaman lafiya a  Mali
Image caption Dakarun kiyaye zaman lafiya a Mali

Wani bam da aka dana shi a mota yayi ta'adi a garin Kidal na arewacin Mali.

Lamarin dai yayi sanadiyyar mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya biyu, wasu kuma sun jikkata.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Senegal ne ke gadin bankin mallakin gwamnati dake Kidal, garin da tawayen Azibinawa 'yan aware ya samo asali shekaru biyu da suka wuce.

An kai harin ne yayinda ake shirin gudanar zabe 'yanmajalisar dokoki zagaye na biyu a kasar ta Mali.

Babu dai wanda ya amsa cewa shi ya kai wannan hari, amma kuma kungiyar 'yan aware ta MNLA mai fafutukar kwatar 'yancin yankin Azawad ta yi kiran da a kaurace ma zaben na gobe.