Gwamnatin Najeriya ki kwashe mu daga Bangui

Sojojin Faransa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Image caption Sojojin Faransa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sakamakon zaman dar-dar da ake yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, 'yan Najeriya a birnin Bangui na kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kwashe su.

Wannan dai ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin kungiyoyin Musulmi da Kirista a Jamhuriyar Afirka Tsakiya.

'Yan Najeriyar na kokawa game da abinda suka ce hallin tsaka mai wuyar da suke ciki na zaman rashin tabbas game da yiwuwar kai musu hare-hare a wuraren da suka samu mafaka kafin a kwashe su zuwa gida.

Bayanai sun ce an kashe 'yan Najeriyar akalla sama da 80 a yayin fafatawa tsakanin kungiyoyin biyu da basa ga maciji da juna a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar.