Ana muhawarar ware mata da maza a Birtania

David Cameron
Image caption David Cameron ya ce bai ga dalilin da zai sa a raba wajen zaman maza da matan ba

Fraiministan Birtaniya, David Cameron, ya sanya baki a wata muhawara da ake yi kan ko jami'o'i za su iya raba maza da mata a wurin lacca idan wani bakon mai gabatar da lacca musulmi ya bukaci hakan.

Wata kungiya da ke wakiltar galibin jami'o'i ta fitar da wasu ka'idoji ne da ake ganin za su haifar da cece-kuce, da ke cewa za a iya raba maza da matan bisa zabi.

To amma shi kuma fraiministan Birtaniyan wanda ya bi bayan wasu manyan 'yan siyasar Birtaniyan ya ce ba daidai ba ne ta ko wana hali a raba maza da mata da ke halartar taro bisa bambancin jinsinsu.

Masu adawa da shirin na ganin cewa abu ne da zai dadada wa masu tsattsauran ra'ayin kishin Islama kawai.

Yanzu dai kungiyar jami'o'in ta ce za ta sake duba tsarin.