Kofin Duniya : Ma'aikata sun mutu a Brazil

Filin Wasan Manaus a Brazil
Image caption Kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa hadarin mutuwar ma'aikacin ba

A Brazil wani ma'aikacin gini da kere-kere ya rasu bayan da ya fado daga rufin wani filin wasa da ake ginawa domin gasar kofin duniya ta kwallon kafa da za a yi a kasar a 2014.

Mutumin ya rikito kasa ne daga tsawon sama da mita 30 yayin da yake aiki a kan rufin sabon filin wasan a birnin Manaus.

Wakilin BBC ya ce kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa hadarin ba, kuma shi ne ma'aikaci na biyar da ya mutu a filayen wasan da ake ginawa na gasar kofin duniyarda za a yi.

Sa'oi kadan bayan mutuwar mutumin wani ma'aikacin shi ma ya rasu a sanadiyyar cutar zuciya a kusa da wani wurin da shi ma ake aikin filin gasar kofin duniyar. Iyalansa sun ce aikin da yake ne ya yi yawa.

Kawo yanzu ma'aikata da dama dai sun mutu a filayen wasan da ake ginawa a Brazil din yayin da kasar ta ke kokarin kammala filayen akan lokaci.