Kumbon China a duniyar wata zai fara aiki

Image caption China ta zama ta uku a duniya da ta tura kumbo duniyar wata

Kumbon da China ta tura duniyar wata ya matsa daga gurbin da ya sauka domin fara gudanar da bincike, sa'oi bayan da Chinan ta zama kasa ta uku da ta tura kumbo duniyar wata.

Kumbon zai yi watanni uku a doron duniyar watan yana tattara bayanan kimiyya yana kuma neman albarkatun da Chinan za ta iya amfani da su wata rana.

Miliyoyin jama'a ne a duniya suka ga hotuna a talabijin na yadda kumbon ya sauka; ciki har da Leo Enright, mai fashin baki da ba da bayanai kan al'amuran sararin samaniya.

Leo Enright ya ce "babu tantama kuma babu tababa china ta yi nasarar sauka da kumbon binciken samaniya a duniyar wata".

Wannan shi ne karon farko tun shekaru 40 da aka tura kumbo duniyar wata, abin da Chinan ke tunkaho da shi.

Karin bayani