'Yan sanda sun kashe dalibi a zanga zangar Kenya

Zanga zanga a Kenya
Image caption Tarzoma a Kenya

A Kenya 'yan sanda sun hallaka wani dalibi yayin wata zanga-zanga a jami'ar Nairobi.

'Yan sandan dai sun yi amfani ne da bindiga wajen tarwatsa gungun wasu dalibai dake zanga-zanga saboda mutuwar wani dalibi da ake zargi da aikata ba daidai ba yayin rubuta jarrawa, a hannun 'yan sanda.

'Yan sanda dai sun ce, dalibin ne ya kashe kansa, amma daliban suka ce, suna kyautata zaton 'yan sanda ne suka lakada masa duka har sai da yace, ga garinku nan.

Daliban na jami'ar Nairobi sun auka wa ofishin 'yan sanda kuma suka kona motoci.