Al-Qaeda ta ce ita ta kai hari Mali

'Yan kungiyar Ansar din a Mali
Image caption Duk da an kawar da su 'yan gwagwarmayar Islaman na kai hare hare a Mali

Reshen kungiyar Al-Qaeda na yankin Afrika ta Arewa ya ce shi ne ya kai harin bam na mota da ya hallaka wasu sojojin Senegal biyu da ke aikin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a garin Kidal a arewacin Mali.

Harin ya kuma jikkata wasu sojojin Mali biyu da wani sojan tabbatar da zaman lafiya daya, lokacin da dan kunar bakin waken ya kaura motar da yake ciki a ginin banki daya tilo da ke aiki a birnin.

Mai magana da yawun kungiyar ta Al-Qaeda a yankin Magrib, Sultan Ould Badi, ya ce harin martani ne ga kasashen Afrika da ke mara baya ga kasar Faransa a yaki da masu gwagwarmayar Islama a Mali.

Dakarun Faransan dai sun yi galaba a kan 'yan tawaye musulmi a arewacin Mali, kusan shekara daya da ta wuce amma har yanzu 'yan tawayen na ci gaba da kai hare hare.