Birtaniya: Daurin rai-da-rai kan fataucin mutane

Image caption Birtaniya ta ce ya kamata a yanke wa masu ci da gumin yara hukuncin daurin rai-da-rai

Gwamnatin Birtaniya za ta wallafa wasu shawarwari da za su ba ta damar aiwatar da hukunci mai tsauri kan mutanen da ke ci da gumin yara da fataucin mutane.

Shawarwarin, wadanda Sakatariyar Gida ta kasar,Theresa May, ta fitar a watan Agusta za su bukaci yin daurin rai-da-rai kan duk mutumin da aka kama da wadannan laifuka maimakon hukuncin shekaru 14 a a baya aka ba da shawarar yi musu.

Misis May ta kuma bukaci a kafa sabuwar hukumar da ke yaki da bautar da mutane.

Rahotanni daga Birtaniya dai sun nuna cewa dubban mutane ne ke fuskanatar bautarwa.

Karin bayani