An sake zaben Michelle Bachelet a Chile

Michelle Bachelet
Image caption Michelle Bachelet Shugabar kasar Chile karo na biyu

A kasar Chile, an zabi 'yar takara ta jam'iyyar 'yan gurguzu Michelle Bachelet a matsayin Shugabar kasar a karo na biyu, bayan ta kayar da abokiyar hamayyarta ta jam'iyyar masu ra'ayin mazan-jiya Evelyn Matthei da ratar kur'u masu yawa.

Ms Matthei din dai har ta rungumi kaddara. Wannan dai shine karo na biyu na zaman Mr Bachelet a matsayin Shugabar kasa. Ita ce ta cinye zaben da aka yi a shekara ta 2006, to amma a karkashin dokar kasar ta Chile dole ta sauka bayan wa'adin mulki na farko.

A yayinda yanzu aka kidaya fiye da rabi na kuri'un da aka kada a zagayen karshe, hukumomin zaben kasar sun ce ta cinye kashi sittin bisa dari na kuri'un.

Wakilin BBC a Santiago ya ce alhaki ya rataya ga wuyan ta na cimma burin ta na kara ma kamfanoni haraji da bayar da ilimi na manyan makarantu kyauta tare da halatta zubar da ciki.

Karin bayani