Japan za ta kara kashe kudade a fannin tsaro

Shinzo Abe
Image caption Japan da China suna jayayya akan wasu tsibirai

Kasar Japan ta ba da sanarwar cewar za ta kara yawan kudaden da take kashewa a fannin tsaro cikin shekaru biyar masu zuwa.

Masu aiko mana labarai sun ce wannan wata alama ce karara, tun lokacin da Firai Minista Shinzo Abe ya karbi ragamar ikon mulki shekara daya da ta wuce Japan din ke neman mayar wa kasar China raddi a kan tsokanar fadan da take mata.

Gwamnatin ta Japan ta ce za ta kashe fiye da dola billiyan dari biyu da talatin cikin shekaru biyar masu zuwa wajen sayen jirage da kayan yaki.

Sanarwar ta baya-bayan nan dai ta zo ne a daidai lokacinda suke jayayya da China ta ikon mulki da wasu tsibirrai dake kudancin tekun Chinar.

Karin bayani