Majalisa za ta binciki zargin Obasanjo

Goodluck da Obasanjo
Image caption Za a gabatar da zarge zargen Obasanjo a gaban majalisa

'Yan majalisar wakilan Nigeria sun ce za su tsige shugaban kasar, Goodluck Jonathan, idan zarge-zargen da aka yi akansa suka kasance gaskiya.

Tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, ya zargi shugaba Jonathan da yunkurin wargaza Nigeria, da sauran zarge-zarge da suka shafi cin hanci da rashawa da nuna kabilanci, lamarin da ya sa jam'iyyar adawa ta APC ta bukaci 'yan majalisar su tsige shi.

Wasu 'yan majalisar wakilan kasar sun shaida wa BBC cewa za su gabatar da batun a zauren majalisar domin yin muhawara.

Sun kara da cewa daga nan ne za su auna nauyin zarge-zargen kuma da zarar sun amince cewa abubuwan da shugaban kasar ya yi sun cancanci a tsigeshi ba za su kasa-a-gwiwa wajen cire shi ba.

Karin bayani