An fara sayar da kwafutar N7,500 a UK

Aakash
Image caption Kwamfutar hannu mafi arha a duniya

Kamfanin Datawind na kasar UK ya fara sayar da kwamfutar hannu samfurin UbiSlate 7Ci akan kudi Naira 7,500 wata £30 na Ingila.

An dai kaddamar da wannan kwamfutar hannun ne a India inda a can ake kiranta Aakash 2 domin taimakawa dalibai amfani da intanet cikin rahusa.

Sai dai manzarta sun ce masu sanyen kwamfutar a UK ba za su ji dadinta ba idan su ka kwatanta da sauran kwamfutocin hannu da ake da su a kasuwa.

Kwamfutar mai fadin inci bakwai ma da RAM mai karfin 512MB, tare da rumbun ajiye mai girman 4GB da kuma wurin zura wayar USB.

Image caption Ranar kaddamar da Aakash a India

Lokacin da aka gabatar da Aakash a India a 2011 an yi mata taken "kwamfutar hannu da aka sarrafata ta hanyar latsa fuskarta mafi arha a duniya" domin amfanin daliban sakandare da jami'a. Fitowar farko bata karbu ba, amma samfaru na biyu mai suna Aakash 2 ta samu kasuwa.

Mutumin da ya kirkiro kamfanin Datawind, Suneet Singh Tuli ya ce babbar manufarsa ita ce samawa masu karamin karfin damar amfani da intanet.

Sai dai wani manzarci kan fasahar intanet Ben Wood ya ce arha ba ta biyan bukata a sha'anin na'urorin kwamfuta. Don haka ba za'a iya kwatanta wannan kwafuta mai arhar tsiya da sauran kwamfutoci masu arha da su ka dara ta kudi ba.

A baya bayan nan dai kamfanoni da dama sun fara sayar da kwamfutocin hannu masu rahusa a UK. Tesco na sayar da ta sa kwamfutar £120 yayin da Argos ke sayar da ta sa akan £100.