Za a kwaso 'yan Najeriya daga Saudiya

'Yan cinrani a Saudi Arabia
Image caption An tsare 'yan Najeriya da dama a Saudiyya

Yayinda hukumomin Saudiyya ke ci gaba da tasa-keyar 'yan ci rani da ba su da takardun iznin zama cikin kasar, gwamnatin Nijeriya ta ce, a karshen makon nan za ta tura jirgin sama da zai kwaso daruruwan 'yan Kasar ta dake Saudiyya wadanda basu da takardun iznin zama a kasar.

Wannan dai shine karon farko da gwamnatin Nijeriyar za ta dauki wannan mataki.

Jakadan Najeriya dake birnin Jeddah na kasar Saudiyya Ambasada Ahmed Umar ya ce ya zuwa yau an kama 'yan Najeriya 951.

'Banda wadanda aka kama, akwai kuma wadanda suka kawo kansu, inda suka nuna bukatar suna son su koma gida' in ji jakadan na Najeriya.

Gwamnatin Saudiya dai ta dauki matakin tuso daruruwan 'yan cirani dake kasar zuwa Kasashensu ne, bayan wa'adin da aka deba masu na su sabunta takardunsu ya cika.

Karin bayani