"Sai an yi zabe a jihohin dokar-ta-baci"

Shugabannin Jam'iyyar APC a Najeriya
Image caption Rashin tsaro ka iya kawo cikas a zabe

A Najeriya jam'iyyar adawa ta APC da gwamnatocin jihohin da ke karkashin dokar-ta-baci sun fara maida martani dangane da furucin da shugaban hukumar zaben kasar ya yi cewa da wuya a gudanar da babban zabe a yankunansu idan yanayin tsaro bai inganta an janye dokar-ta-bacin ba.

Jam'iyyar APC ta ce da ma can ta na da shakku dangane da gaskiyar dukufar gwamnatin tarayya wajen yaki da maharan da ke tada zaune tsaye a jihohin.

Gwamnatocin jihohin Borno da Yobe da Adamawa sun ce rashin gudanar da zabe a jihohin tamkar sallama yankin ne ga kungiyar Boko Haram, yayin da a bangare guda kuma suke zargin gwamnatin tarayya da kokarin hana musu shiga zabe kasancewar jihohinsu karkashin mulkin jam'iyyar adawa.

Duk da irin caa da gwamnatocin jahohin uku da kuma jam'iyyar APC suka yi, za a iya cewa kokari suke yi na yi wa tubkar-hanci ko riga kafi, saboda Shugaban hukumar zaben bai ce ba za a yi zabe a jihohin ba.

Abinda ya ce lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban majalisar dattawan Najeriya, shi ne idan har yanayin tsaro bai inganta ba, kuma wadannan jihohi uku na karkashin dokar-ta-baci har zuwa lokacin da za'a gudanar da babban zaben kasar, to doka ba ta ba da damar yi ba.