An sami karuwar noman tabar wiwi a Burma

Image caption Bayan Afghanistan, Burma ce ta biyu wajen noman wiwi

Majalisar dinkin duniya ta ce an samu matukar karuwar noman tabar wiwi a Myanmar a wannan shekarar.

Ta ce, an gaza, a yunkurin hana girbin ta a hukumance saboda manoman ba su da wata hanyar samun abinci.

Hukumar Majalisar dinkin duniya mai yaki da miyagun laifukka da kwayoyi ta yi kiyasin cewa Myanmar din, wadda aka fi sani da Burma, za ta samar da ton dari takwas da saba'in na tabar ta wiwi a shekara ta 2013, abinda zai sanya ta zama kasa ta biyu mafi girma a duniya dake noman tabar bayan Afghanistan.

Majalisar dinkin duniya ta yi nuni da karuwar bukatar taabar ta wiwi a yankin da kuma rashin wasu nau'in abinci da za a iya nomawa a sayar a yankin mai tsaunuka na arewa maso gabashin Burma a matsayin dalilan da suka sa aka samu habakar noman taabar ta wiwi.

Karin bayani