Rasha za ta bai wa Ukraine dala biliyan 14

Image caption 'Yan kasar Ukraine sun kwashe kwana da kwanaki suna zanga-zanga

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wa Ukraine tayin dala biliyan sha hudu da kuma ragin kashi talatin cikin dari na farashin makamashi domin hana ta fadawa rikicin tattalin arziki.

Mista Putin ya yi wannan sanarwa ne a Moscow, inda takwaransa Vikor Yunokovych ya kai masa ziyara tare da neman agajin kudade.

Sai dai yace ba su tattauna game da wata dangantaka ta kut-da-kut ba tsakanin kasashen biyu ba.

Mista Putin ya kara da cewa tattauna kan batun shigar Ukraine kungiyar fasa kwaurin Rasha ba wadda kasashen Belarus da Kazakhstan ke ciki ba.

Daruruwan masu zanga-zanga ne a makwannin da suka wuce ke matsawa gwamnatin shugaba Yunokovych lamba, tare da bukatarsa da ya nemo taimakon kudade daga kasashen yammacin duniya da kuma kulla danganta da tarayyar turai.

Karin bayani