An kai hukumar tsaron Amurka kotu

Shugaba Barack Obama na Amurka
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Daya daga cikin mutane biyu da suka gurfanar da hukumar tsaron kasa ta Amurka gaban Kotu don kalubalantar karbar bayanan wayoyin da aka yi na layukka masu dimbin yawa ya ce hukumomin tsaron suna da masaniyar cewa abinda suka yi ya saba ma doka.

Larry Klayman yana magana ne da BBC bayan wani Alkali na Kotun Tarayya Richard Leon ya yanke hukuncin cewa tseguntawar da tsohon jami'in leken asirin nan na Amurka Edward Snowden ya yi kan batun, lamari ne da ya saba ma tsarin mulkin kasar.

Alkalin Leon ya yanke hukunci na share fage da ya haramta cigaba da karbar irin wadannan bayanai, amma bai yanke hukunci kan shari'ar ba, har sai lokacinda gwamnatin Amurka ta daukaka kara.