Za a soma taro akan dokokin Bankunan Turai

Image caption Za a gudanar da Taron a Brussels

Shugabannin Kasashe 28 da suka kafa Tarayyar Turai za su fara wani taro a Brussels yau, kuma babban abinda za a tattauna akai shine sabbin dokokin tafiyar da bankuna a yankin Turan.

A ranar Laraba ne dai, Ministocin kudi na Tarayyar Turai suka cimma matsaya a kan tsarin dokokin da za a yi amfani da su wajen tafiyar da bankuna na yankin Turai.

Yarjejeniyar za ta ba da daamar kirkirar wata sabuwar hukuma da za ta zamo da karfin iko na rufe bankunan da suka gaza don kaare su daga afkawa matsaloli na rashin kudi kamar yadda lamarin ya faru a Cyprus da Ireland da Spain.

Ministocin sun rigaya sun amince da hanyoyin da za a dauki nauyin wannan tsari don tabbatar da cewa nauyin farfado da bankunan bai fada kan masu biyan haraji ba.

Karin bayani