An ci tarar N100,000,000 kan hakkin mallaka

Image caption Dubunnan mutane ne ke dora fina-finai a intanet ba bisa ka'ida ba.

An ci tarar wani dan Sweden mai shekaru 28 Krona miliyan 4.3 daidai da Naira miliyan 100 saboda dora wani fim guda daya a intanet wanda bai mallaki hakkin mallakarsa ba.

An kuma yanke masa hukuncin aikin al'umma na sa'o'i 160 saboda dora wasu fina-finan 517.

Kungiyar yaki da masu keta hakkin mallaka Rights Alliance ta bayyana mutumin a matsayin wanda yafi kowa keta hakkin mallaka a Sweden.

Sai dai jam'iyyar masu keta hakkin mallaka ta Sweden ta ce hukuncin ya yi tsauri, ta kuma nemi a yi wa dokokin kare hakkin mallaka garambawul.

Diyyar asara

Kamfanin Nordisk Film AS - wanda ya mallaki fim din da mutumin ya sa a intanet ya kididdige asarar da ya ce ya yi sanadiyyar rarraba fim din ba da izini ba.

Sauran kamfanonin da suka mallaki fina-finai 517 da mutumin ya sa ba su kididdige ta su asarar ba, shi ya sa ba'a biya su diyya ba.

Kungiyar Rights Alliance mai rajin kare hakkin mallaka a Sweden ta ce: "mafi yawan adadin tarar za'a ba da shi ne a matsayin diyya ga kamfanin da abin ya shafa."

Kungiyar ta ce za ta ci gaba da gurfanar da wasu masu keta hakkin mallakar gaban kuliya nan ba da jimawa ba.