Mutane 23 sun mutu a hadarin mota a Kano

Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso
Image caption An binne mutanen da suka mutu a inda akai hatsarin

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria sun ce mutane 23 sun mutu sakamakon wani hadarin mota da ya rusta da su a garin Takai dake karamar hukumar ta Takai dake gabashin jihar.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba da rana inda wata babbar mota dake dauke da mutanen ta fadi, ta kuma kama da wuta, abinda ya yi sanadiyyar konewar mutane 22 kurmus a nan take, yayinda karin guda kuma ya mutu a asibiti.

An dai binne mutanen a wajen da lamarin ya faru.

Hukumar kare hadura ta kasar ta tabbatarwa BBC afkuwar lamarin, inda ta ce ta na kyautata zaton fashewar taya ce ta haddasa hadarin.

A Najeriya dai ana danganta yawan aukuwar hadura sakamakon rashin kyawun tituna da kuma tukin ganganci daga direbobi.

Karin bayani