Masar na zargin Morsi da ta'addanci

Image caption Hambararren shugaban Masar Muhammad Morsi.

Mai shigar da kara na gwamnatin Masar ya bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban kasa Muhammad Morsi da fitattun masu kishin Islama 34 bisa zargin hada baki da kungiyoyin kasashen waje domin tada hankali da aiwatar da ta'addanci a Masar.

Mai shigar da karar ya ce kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta aiwatar da ta'addanci a Masar tare da kulla wani shirin ta'addanci da ya kunshi alaka da kungiyar Hamas ta Palasdinu da Hezbollah ta Lebanon.

Dama dai ana tuhumar Mr Morsi da laifin iza wutar rikici lokacin zanga-zangar da aka gudanar sa'adda ya na kan mulki.