Sudan ta Kudu na fuskantar yakin basasa

'Yan gudun hijira na Sudan ta Kudu
Image caption Mutane suna tserewa daga Sudan ta Kudu saboda rikici

Shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Gerard Araud ya ce rikicin da ake yi a Sudan ta Kudu wanda ake ganin na kabilanci ne zai iya jefa kasar yakin basasa.

Mr Araud ya gaya wa BBC cewa Majalisar Dinkin Duniya ta samu rahotannin daruruwan mutane sun mutu tun lokacin da aka yi yunkurin juyin mulki a kasar a ranar Lahadi, kodayake ya ce, fadan bai cika shafar farar hula ba.

Ya ce wasu mutanen kimanin 20,000 sun nemi mafaka a harabar ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Juba babban birnin kasar kuma magunguna da abincin da majalisar ke da su na kula da dimbin mutanen na neman kaarewa.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya dora laifin yunkurin juyin mulkin kan sojojin dake biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Marchar wanda ba dan kabilarsu ba ne.

Karin bayani