An bude bankin shanu a Zimbabwe

Image caption Kananan manoman Zimbabwe na dogaro ne da shanunsu.

Wani sabon banki a karkarar Zimbabwe ba shi da na'urar sanyaya daki ko jami'ai sanye da kwat - sai kashin shanu da 'yan kwadago sanye da kayan aiki.

Rassansa ma gonaki ne kuma jami'ansa kan fita ne da kansu domin karbo ajiya daga abokan huldarsu.

Daya daga cikin abokan huldar, Stephen Chikoto, karamin manomi a kauyen Zvishavane mai nisan 390km kudu da Harare, babban birnin kasar, ya ba da ajiyar shanunsa guda tara.

Jami'an ma'aikatar gona kan kimanta kudin dabbar sannan su mikawa mai ajiyar satifiket na adadin abinda ya ajiye.

Yara za su makaranta

Tsarin dai ya tanadi cewa mai ajiyar zai bar dabbobinsa cikin asusun tsawon akalla shekaru biyu, inda bankin zai cigaba da kiwata su tare da kula da lafiyarsu.

Bankin zai kuma biya mai ajiyar kudin ruwan 10% a kowacce shekara, sannan kuma za'a iya amfani da satifiket din wurin neman rance.

Jami'in bankin Charles Chakoma ya ce kananan manoman Zimbabwe sun mallaki shanu fiye da miliyan uku da kimarsu ta kai $1bn.

Mr Chakoma ya ce tsarin zai sauke nauyin kiwo daga kan kananan yara abin da zai ba su damar zuwa makaranta.

Sai dai manazarta tattalin arziki irinsu Christopher Mugaga na ganin beken tsarin, inda ya ce kamata ya yi gwamnatin Zimbabwe ta mai da hankali kan inganta noma don kudi ba wai batun kananan manoma ba.