An samu wadanda suka kashe Rigby da laifi

Image caption Michael Adebolajo da Michael Adebowale jim kadan bayan kashe Lee Rigby a Woolwich, London.

An samu wasu masu kishin Islama 'yan Britaniya su biyu da laifin kashe wani soja da rana tsaka a birnin London.

A cikin mintuna 90 kacal, masu taya alkali yanke hukunci suka tabbatar da cewa Michael Adebolajo da Michael Adebowale sun kashe Fusilier Lee Rigby daura da wata barikin soji a watan Mayu.

Kotun ta ji cewa mutanen biyu sun kade sojan da mota ne lokacin da yake tsallaka titi sannan suka yi yunkurin datse masa kai.

Wadanda abin ya afku a gabansu sun dauki hotunan mutanen biyu suna bayanin cewa su sojojin Allah dake daukar fansa kan laifuffukan da Britaniya ke yi a kasashen Musulmi.